Kotun ICC Ta Samu Kwamandan LRA Na Uganda Da Tabka Laifuffukan Yaƙi

2021-02-04 20:32:25
Kotun ICC Ta Samu Kwamandan LRA Na Uganda Da Tabka Laifuffukan Yaƙi

Kotun ƙasa da ƙasa mai shari’ar manyan laifuffukan yaƙi ICC ta samu tsohon kwamandan ƙungiyar nan ta Lord’s Resistance Army (LRA) ta ƙasar Ugandan Dominic Ongwen da laifin tabka laifuffukan yaƙi da kuma take haƙƙoƙin bil’adama.

A yau Alhamis ne dai kotun da ke birnin Hague na ƙasar Netherlands ta sami Dominic Ongwen ɗan shekaru 45 a duniya da laifi kan laifuffuka guda 61 da take zarginsa da su da suka haɗa da kisan gilla, yin fyaɗe na gama-gari, bautar da mata, sace ƙananan yara, azabtarwa, ƙona gari da dai sauransu da ake zargin ya aikata a a farko-farkon shekarun 2000s.

Alƙalan kotun sun ce Mr. Ongwen ya aikata waɗannan ayyuka ne a tsakanin shekarun 2002 da 2005 bisa raɗin kansa ba tare da an tilasta masa ba. Don haka an tabbatar da laifinsa ba tare da wani tantama ba inji babban alkali mai shari’ar Bertram Schmitt yayin da ya ke karanta hukunci.

Duk da cewa alkalan dai ba su faɗi hukuncin da aka yanke masa ba, sai wani lokaci a nan gaba, amma dai ana ganin za a iya yanke masa hukuncin zaman gidan yari har na tsawon rayuwarsa saboda girman laifuffukan da ya aika ɗin.

Kungiyar 'yan tawayen LRA dai ta shafe kusan shekaru 20 ta na gudanar da ayyukanta a arewacin kasar Uganda. A baya dai kungiyar ta yi kaurin suna wajen kona wasu kauyukan kasar, da sace mata da kuma maza matasa, da kona kauyuka.

A shekarar 2015 ne dai Dominic Ongwen ya mika wuya a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, inda mafi yawan 'yan tawayen LRA ke da sansani.

Dominic Ongwen ya zama sojan 'yan tawaye ne tun yana yaro karami bayan sace shi da ‘yan tawayen suka yi inda sannu a hankali har ya zama babban mukarrabin jagoran kungiyar LRA, Joseph Kony.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!