​Faransa: Ana Rufe Shagunan Musulmi Bisa Zarginsu Da Alaka Da Masu Tsatsauran Ra’ayi

2021-02-04 14:54:29
​Faransa: Ana Rufe Shagunan Musulmi Bisa Zarginsu Da Alaka Da Masu Tsatsauran Ra’ayi

Gwamnatin kasar Faransa ta rufe daruruwan shagunan musulmi bisa zarginsu da alaka da masu tsatsauran ra’ayi, ko kuma bisa wasu dalilai na saba ka’idar mallakar wuri haya.

Rahotanni daga kasar ta Faransa sun ce, cibiyar da aka kafa domin sanya ido a kan musulmi wadda ke karkashin ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar ta Faransa, ta rufe shaguna fiye da dari hudu tun bayan kafa a cikin watan Janairun shekara ta dubu biyu da ashirin.

Gwamnatin kasar ta Faransa ta kafa wannan hukuma ne domin sanya ido a kan dukkanin harkokin musulmi a kasar, lamarin da yake takura wa musulmin a cikin harkokinsu na rayuwa ta yau da kullum a kasar.

Daga cikin matakan baya-bayan nan da hukumar ta dauka shi ne rufe daruruwan shagunan musulmi da kuma wurarensu na cin abinci, inda musulmi sukan samar da wurare na musamman domin sayar da abinci na halal a kasar.

Daya daga cikin ma’aikatan wannan cibiya da ke sanya ido a kan musulmi a karkashin ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Faransa da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa wasu kafofin yada labarai cewa, an umarce su das u rufe wasu wurare na musulmi a cikin birnin Paris ko ta wace hanya, ba tare da musulmin sun saba wa wata ka’ida ko doka ba.

A bisa kididdigar da aka gudanar a cikin shekara ta 2016, yawan musulmi mazauna kasar Faransa ya kai miliyan miliyan biyar da digo bakwai, wato kashi takwas da digi takwas cikin dari na dukkanin al’ummar kasar.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!