CHAN 2020 : Morocco Da Mali Zasu Fafata A Wasan Karshe

2021-02-04 09:45:52
  CHAN 2020 : Morocco Da Mali Zasu Fafata A Wasan Karshe

A gasar cin kofin Afrika, na ‘yan wasan dake buga kwallo a gida, ta CHAN 2020, dake gudana a kasar Kamaru, kasashen Mali da Morocco, sun ciri tikitan zuwa wasan karshe na gasar.

A wasan da suka guda jiya Laraba, Mali ta dauke Guinea da kwallo 5-4 a wasan daga kai sai mai tsaron gida, bayan sun tashi kunnen doki ba tare da zura kwallo ba a mintunan da aka kayyade har zuwa karin lokaci.

Ita kuwa Morocco ta lallasa Kamaru mai masaukin baki da ci 4 da nema a wasan da suka buga a jiyan.

A ranar Asabar za’a kara tsakanin kasashen Guinea Da Kamaru sun domin neman matsayi na uku.

Yayin da a ranar Lahadi za’a fafata tsakanin Mali da Morocco mai rike da kofin a wasan karshe na gasar ta CHAN 2020.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!