Netanyahu Ya Dakatar Da Ziyarar Da Zai Kai A Bahrain Amma Zai Ziyarci UAE

Firayi ministan Isra’ila Benjamin
Netanyahu ya janye ziyarar da ya shirya gudanarwa a kasar Baharain a cikin
wannan wata na Fabrairu.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun
bayar da rahotanni cewa, gwamnatin Isra’ila ta sanar da janye ziyarar da Benjamin
Netanyahu ya shirya gudanarwa a Bahrain, amma zai ziyarci hadaddiyar daular
larabawa.
Bisa tsarin da aka yi tun daga farko
dangane da ziyarar, Netanyahu zai ziyarci Bahrain da UAE, amma yanzu an janye
ziyararsa a Bahrain, inda zai ziyarci UAE, kuma zai yi sa’oi uku ne kawai a
birnin Abu Dhabi a ranar 9 ga wannan wata na Febrairu, sannan koma Tel Aviv,
sabanin shirin da aka yi kan cewa zai kwashe tsawon kwanaki uku a UAE.
Baya ga haka kuma Netanyahu zai tsaya a birnin Abu Dhabi ne
kawai, maikon ziyartar wasu garuruwan da suka hada da birnin Dubai babbar
cibiyar kasuwanci ta kasar UAE.
Wannan dai shi ne karon farko da
gwamnatin Isra’ila take sanar da ziyarar firayi ministanta a hukumance zuwa wata
kasa daga cikin kasashen larabawa.
015