​Zarif Ya Gana Da Shugaban Kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan

2021-01-30 10:23:25
​Zarif Ya Gana Da Shugaban Kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif, a daren jiya Juma’a ya gana da shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan a birnin Ankara.

A cikin wani bayani da ya rubuta a shafinsa na twitter, Zarif ya bayyana cewa, ya gudanar da tattaunawa mai armashi tare da shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan a kan batutuwa daban-daban, wadanda suka shafi alaka tsakanin Iran da Turkiya, da kuma sauran batutuwa na yankin da ma na kasa da kasa.

Zarif gwamnatocin Iran da Turkiya suna da mahanga guda a kan wajabcin yin aiki tare domin warware matsaloli da suke ci ma al’ummomin yankin tuwo a kwarya, ba tare da yin katsalandan daga kasashen ketare ba.

Ya ce kasashen Turkiya da Iran suna yin aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya a Syria, kamar yadda kuma suna da irin wannan mahangar dangane da abin da ya shafi yankin Karabakh, inda suka taka muhimmiyar rawa wajen ganin an tsaida yakin da ya barke tsakanin Azarbeijan da kuma Armenia.

Zarif ya kammala ziyarar da ya gudanar a cikin wannan mako, wadda ta kunshi kasashen Azarbeijan, Rasha, Armenia, Georgia da kuma Turkiya.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!