​Zarif:Bukatar Amurka Dangane Da Shirin Nukliyar Kasar Iran Ba Za Ta Taba Samuwa Ba

2021-01-29 20:45:47
​Zarif:Bukatar Amurka Dangane Da Shirin Nukliyar Kasar Iran Ba Za Ta Taba Samuwa Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa bukatar Amurka dangne da shirin nukliyar kasar Iran ba za ta taba samuwa ba.

Kamfanin dillancin labaran Anatoly na kasar Turkiya ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a , a lokacinda yake gabatar da taron ‘yan jaridu na hadin guiwa da tokoransa na kasar Turkiyya Mevlut Cavusoglu a birnin Istambul.

A ranar laraban da ta gabata ce dai, sabon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya bayyana cewa Amurka ba za ta koma cikin yarjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA ba, sai in har Iran ta koma kan yadda take kafin Amurka ta fice daga yar jejeniyar.

A halin yanzu dai kasar Iran tana tace sinarin yuranium har zuwa kashi 20% wanda ya dara abinda yake cikin yarjejeniyar JCPOA, saboda ta jawo hankalin Amurka ta dawo cikin yarjejeniyar.

Tsohun shugaban kasar Amurka Donal Trump ne ya fice daga yarjejeniyar ya kuma dorawa kasar Iran takunkuman tattalin arzi mafi muna, da nufin tilasta mata sake dawowa kan teburin tattaunawa ko kuma gwamnatin kasar ta rushe. Bukatar da Trump bai samu ba har wa’adin gwamnatinsa ya shude.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!