​Iran: Amurka Ce Ta Karya Alkawarinta Karkashin Kudurin MDD Mai Lamba 2231 Na Kwamitin Tsaro Dangane Da Yarjejeniyar JCPOA

2021-01-28 13:21:20
​Iran: Amurka Ce Ta Karya Alkawarinta Karkashin Kudurin MDD Mai Lamba 2231 Na Kwamitin Tsaro Dangane Da Yarjejeniyar JCPOA

Kakakin tawagar kasar Iran a MDD ya maida martani wa sabon sakaren harkokin wajen kasar Amurka dangane da yarjejeniyar nukliyar kasarsa. Ali Reza Mir-Yusufi ya bayyana cewa Amurka ce ta fice daga yarjejeniyar JCPOA sannan ta yi watsi da kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231 wanda ya tabbatar da yarjejeniyar, don haka dole ne Amurka ta daukewa kasar takunkuman da ta dora kasar sannan ta koma cikin yarjejeniyar.

Mir-Yusufi ya ce har yanzun Iran bata sabawa yarjejeniyar JCPOA , don maadda ta 36 na yarjejeniyar ce ta bata damar rage hadin kai da take yi don tilastawa dayan bangaren dawowa kan yarjejeniyar.

Kafin haka dai sabon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya bayyana a safiyar yau Alhamsi kan cewa Amurka ba zata dagewa kasar Iran takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar ba, sai idan ta koma kan yadda take kafin Amurka ta fice daga yarjejeniyar a shekara ta 2018.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!