Nigeria: An Sami Karin Mutane 1,267 Wadanda Suka Kamu da Cutar Korona A Cikin Sa’o’ii 24 Da Suka Gabata

2021-01-27 09:15:43
Nigeria: An Sami Karin Mutane 1,267 Wadanda Suka Kamu da Cutar Korona A Cikin Sa’o’ii 24 Da Suka Gabata

Cibiyar hana yaduwar cututtuka a tarayyar Najeriya (NCDC) ta bada sanarwan cewa ta gano mutane 1,267 wadanda suka kamu da cutar korona a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Jaridar Nigerian Tribune ta bayyana cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar tun bayan bullarta a farkon shekarar da ta gabata ya kai mutane 124,263.

Labarin ya nakalto shafin cibiyar ta NCDC yana fadar haka a jiya Talata ya kuma kara da cewa an gano wadanda suke dauke da cutar ta korona ne a cikin jihohi 25 na kasar, daga ciki har da birnin Lagos babban birnin kasuwancin kasar, wanda kuma yake gaba da mutane 478, sai kuma Abuja babban birnin Taryyar kasar tare da mutane 211.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!