​Iran: Hannayenmu A Buɗe Suke Ga Saudiyya Matuƙar Ta Sauya Siyasa Da Mu’amalarta

2021-01-25 17:49:35
​Iran: Hannayenmu A Buɗe Suke Ga Saudiyya Matuƙar Ta  Sauya Siyasa Da Mu’amalarta

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Iran ya bayyana cewar hannayen Iran a buɗe suke ga Saudiyya matuƙar dai ta sauya mu’amala da halayenta sannan kuma ta yi watsi da siyasarta na doyon bayan tashin hankali da kuma barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin nan.

Saeed Khateb Zadeh, Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a ganawar da ya saba yi mako-mako da manema labarai, inda yayin da yake magana dangane da siyasar ƙasar Saudiyya da kuma alaƙa da ita, inda yace siyasar Iran dangane da ƙasashen duniya guda ɗaya ce ita ce ƙoƙari wajen samar da hanyoyin da za a tabbatar da kyakkyawar alaƙa da kuma aiki tare tsakanin ƙasashen yankin don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Don haka sai ya ce har ya zuwa yanzu wannan itace siyasar Iran kuma ba ta sauya ba. Kakakin ya ƙara da cewa hannayen Iran a buɗe suke ga Saudiyya matuƙar ta yi watsi da siyasarta na haifar da fitina da tashin hankali a yankin wanda ya ce har yanzu ba ta haifar mata da ɗa mai ido ba.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan harin ta’addancin baya-bayan nan da aka kai birnin Bagadaza na ƙasar Iraƙi kuwa, Mr. Khatebzadeh yayi Allah wadai da hakan yana mai cewa akwai wasu hannaye daga waje da suke ƙoƙarin sake dagula lamurra a ƙasar Iraƙin, sai dai ya ce Iran ba za ta taɓa wasu ƙasashen da ke makwabtaka da Iraƙin su sake dawo da ƙungiyar ta’addancin nan ta Daesh zuwa ƙasar ba.


015


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!