Iraki:Wani Bom Ya Sake Tashi A Birnin Bagdaza, Amma Bai Kashe Kowa Ba
2021-01-25 09:05:19

Wani bom ya sake tashi a wani wuri a cikin babban birnin kasar Iraki Bagdaza kwanaki uku kacal da hare-haren farko a ranar Alhamis da ta gaba, hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 32 da kuma raunta wasu da dama.
Wani wanda yayi wa tashar talabijin ta Al-sumaria magana, wanda kuma baya son a bayyana sunansa ya ce bom din na jiya Lahadi ya tashi ne a yankin Adle amma bai kashe kowa ba.
Harin ranar Alhamis dai shi ne mafi muni da ya auku a kasar ta Iraki tun fiye da shekaru 3 da suka gabata. Kungiyar yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin kashe mutane a harin ranar Alhamis a wata kasuwa wacce ake kira maidan Tayaran.
Banda haka kungiyar ta Daesh ta kashe dakarun Hashdushaabi 11 a garin Tikrit na Lardin salahuddin kusa da birnin Bagdaza a daren Jumma’a. Mayakan Hashdushaabi dai sune suka maida ikon gwamnatin kasar ta Iraki a yankunan da Daesh ta mamaye a shekara ta 2014.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!