Zarif: Kasashen Yankin Tekun Farisa Suna Bukatar Tattaunawa A Tsakaninsu

2021-01-25 08:56:41
Zarif: Kasashen Yankin Tekun Farisa Suna Bukatar Tattaunawa A Tsakaninsu

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa akwai bukatar tattaunawa tsakanin kasashen yankin Tekun Farisa a tsakaninsu don amincewa da juna.

Majiyar muryar JMI ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya da dare a lokacinda yake bankwana don fara ziyarar aiki a kasar Azarbajan.

Labarin ya kara da cewa bayan isarsa birnin Baku na kasar Azerbajan. Zarif ya bayyana cewa ziyararsa kara dankon zumunci ne tsakanin kasashe kawaye da kuma makobtan kasar Iran ne.

Ana saran Zarif zai gana da shugaban kasar Azerbajan Ilham Aliyuf da kuma tokoransa na kasar Jeehun Bairomuf a safiyar yau Litinin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!