ECOWAS Za Ta Tsaida Farashin Gwajin Cutar Korona A Dala 50

2021-01-24 21:51:14
ECOWAS Za Ta Tsaida Farashin Gwajin Cutar Korona A Dala 50

Kasashe mambobin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin AFrika na ECOWAS, sun cimma wata matsaya ta samar da farashi mai sauki na gwajin cutar korona domin baiwa jama’ar yankin yin tafiye tafiye cikin sauki.

Kasashen dai na tunanin amince farashin yin gwajin cutar na PCR ga dalar Amurka 50.

Da yake sanar da hakan shugaban kwamitin kungiyar ta ECOWAS, a wani taron manema labarai ta kafar bidiyo, Jean-Claude Brou, ya ce duba da yadda farashin yin gwajin cutar ta korona ya bambanta tsakanin kasashen mambobin, za’a saukaka farashin ta yadda matafiya zasu fahimci ina aka dosa.

A kasashe kamar su Najeriya da Ghana akan yi gwajin cutar korona a dalar Amurka 150, wanda kuma matsala ce matafiya ganin cewa ana bukatar yin gwajin zuwa da dawowa.

Wannan ne ya sanya ECOWAS, ke son tsaida farashin gwajin zuwa dalar Amurka 50 a tsakanin kasashe mambobinta 15.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!