Tunis: Ana Ci Gaba Da Tashe-Tashe Hankula A Tsakanin ‘Yansanda Da Masu Zanga-Zanga

2021-01-24 14:06:35
Tunis: Ana Ci Gaba Da Tashe-Tashe Hankula A Tsakanin ‘Yansanda Da Masu Zanga-Zanga

Jami’an tsaro a birnin Tunis babban birnin kasar Tunisia suna ci gaba da fafatawa da masu adawa da gwamnatin kasar a kan titin Habib Bogiba a ko wane dare na kimani makonni uku kenan.

Tashar talabijin ta Al-Mayadeen wacce take watsa shirye-shiryenta da harshen larabci a birnin Beirut na kasar Lebanon ta bayyana cewa ya zuwa yanzu an kama mutane kimani 600 daga cikin masu zanga-zangar.

Shekaru goma da suka gabata ne mutanen kasar ta Tunisia suka kori tsohon shugaban kasar Zainul Abidina bin Ali saboda zalunci da kuma rashin samarwa matasa aikin yi.

‘Yan siyasa a kasar ta Tunisia sun bayyana cewa, an yi juyin juya hali a kasar shekaru 10 da suka gabata, amma har yanzun babu rabon arzikin kasar cikin adalci a tsakanin yan kasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!