Sojojin Uganda Sun Ce Sun Kashe Mayaƙan Al-Shabab 189 A Ƙasar Somaliya

Sojojin Uganda da suke aiki da cikin rundunar tabbatar da zaman lafiya na ƙungiyar Tarayyar Afirka a ƙasar Somaliya sun ce sun hallaka mayaƙan ƙungiyar ta’addancin nan ta Al-Shabab a wani harin da suka kai wasu daga cikin sansanoninsu.
A
cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojan Ugandan ta ce a wani
harin da sojojinta suka kai wata maɓuyar
mayaƙan na Al-Shabab a ƙauyukann Sigagle, Adimole da Kayitov da suke kimanin kilomita 100 kudu maso yammacin
birnin Mogadishu babban birnin ƙasar Somaliyan, sojojin sun sami nasarar
hallaka ‘yan ƙungiyar da ke da alaƙa da ƙungiyar ta’addancin nan ta Al-Qaeda su
189 bayan ga lalata makamai da sauran kayayyakin aikin da ‘yan ta’addan suke
amfani da su.
Kakakin
sojin Ugandan Laftanar Kanar Deo Akiiki ya ce an yi amfani da sojojin ƙasa da
kuma kai hare-hare ta sama yayin waɗannan
hare-hare da aka kai wa ‘yan ta’addan, yana mai cewa wannan shi ne adadi
mafi yawa na ‘yan ƙungiyar Al-Shaabab ɗin
da aka kashe a rana guda.
Har
ya zuwa yanzu dai ‘yan ƙungiyar ta al-Shabab ba su ce komai ba dangane da
wannan ikirari na sojojin Ugandan.
Sama
da shekaru 10 kenan sojojin Ugandan suke aiki tare da dakarun tabbatar da zaman
lafiya na ƙungiyar Tarayyar Afirka a ƙasar Somaliyan (AMISOM), wanda babban
manufar tawagar ita ce taimako da kuma goyon bayan gwamnatin tsakiya ta Somaliya da kuma daƙile ƙoƙarin da ƙungiyar ta’addancin ta
Al-Shabab take yi na kifar da gwamnatin.
Cikin ‘yan kwanakin nan dai mayaƙan al-Shabab ɗin sun matsa ƙaimi wajen kai hare-hare kan jami’an tsaro a daidai lokacin da dakarun ƙungiyar Tarayyar Afirka da suke Somaliyan da kuma sojojin ƙasar suke ci gaba da korar ‘yan ta’addan daga tungayensu.