Real Madrid Ta Sake Tabbatar Da Kanta A Matsayi Na Biyu A La Liga Bayan ta Lallasa Alaves Da 4-1

2021-01-24 09:15:58
Real Madrid Ta Sake Tabbatar Da Kanta A Matsayi Na Biyu A La Liga Bayan ta Lallasa Alaves Da 4-1

Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Real Madrid ta sake tabbatar da kanta a matsayi na biyu a wasan league na ƙasar Spain, La Liga, bayan ta lallasa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Alaves ta ci 4-1.

Ƙungiyar Real Madrid ɗin wacce take tsananin buƙatar nasara a wasan, ta zura ƙwallon farko ne a mintuna na 16 da fara wasan bayan da ɗan wasanta Casemiro ya jefa ƙwallo a ragar Alaves, kafin daga baya kuma Karim Benzema ya jefa ƙwallon na biyu a ragar masu masaukin baƙin a mintuna na 41 da fara wasan.

Ana dab da za a tafi hutun rabin lokaci ne kuma ɗan wasan gaba na Real Madrid ɗin Eden Hazard ya jefa ƙwallo ta uku a ragar Alaves.

Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Alaves ɗin ta farke guda daga cikin ƙwallayen lokacin da ɗan wasanta mai suna Joselu ya jefa kwallo a ragar Real Madrid din a minti na 59 da fara wasan.

Daga ƙarshe dai Benzema ya rufe wasan inda ya ci kwallonsa na biyu kana kuma na huɗu na ƙungiyar tasa a minti na 70 da fara wasan.

A halin yanzu dai Real Madrid ɗin ita ce ta biyu a kan jadawalin gasar na La Liga a bayan ƙungiyar kwallon ƙafa ta Atletico Madrid.

Wannan nasarar dai za ta ɗan rage matsin lambar da mai horar da ‘yan wasan na Real Madrid, Zinedine Zidane bayan cire ƙungiyar da aka yi da gasanni guda biyu na ƙasar Spain.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!