Araqchi: Babu Batun Tattaunawa Kan Makaman Iran Masu Linzami

Mataimakin ministan harkokin wajen
kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewa, babu batutun tattaunawa da
wani ko wata kasa kan makaman Iran masu linzami.
A zantawarsa da jaridar L’arpublica
mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana
cewa, a halin yanzu Iran tana jiran kamun ludayin sabon shugaban kasar Amurka
Joe Biden dangane da kurakuran da Trump ya tafka dangane da Iran, shin zai
dauki matakan gyara ne, ko kuwa shi ma zai bi sahun wanda ya gabace shi ne.
Ya ce kasar Iran ba ta gaggauwa
dangane da duk wata tattaunawa tsakanin da Amurka, hakan ba shi daga cikin
muhimman abubuwa a wurinta, abin da yake da muhimmanci shi ne Amurka ta janye
dukkanin takunkuman zalunci da Trump ya dora mata, sannan Amurka ta koma cikin
yarjejeniyar nukiliya kuma ta yi aiki da dukkanin abin da ta rattaba hannu a
kansa.
Dangane da batun shirin na makamai
masu linzami da Iran take kerawa kuwa, Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewa,
wannan shiri ne na kariya, wanda Iran ba za ta taba shiga wata tattaunawa da
wani ko wata kasa kan hakan ba.
A lokacin da aka tambaye kan yiwuwar tattaunawa tsakanin Iran da kasashen yankin tekun fasha, ya bayyana cewa har kullum suna maraba da duk wani abin da zai kara kawo fahimtar juna da yin aiki tare tsakanin dukkanin kasashen yankin, domin hakan zai kara karfafa su, kamar yadda kuma zai karfafa sauran kasashen musulmi a duniya baki daya.
015