An Sanar Da Lokacin Fara Shari’ar Hukunta Trump A Majalisar Dattawan Kasar Amurka

2021-01-23 14:33:56
An Sanar Da Lokacin Fara Shari’ar Hukunta Trump A Majalisar Dattawan Kasar Amurka

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawan Amurka ya sanar da cewa a wata mai kamawa na Fabrairu ne za a fara shari’ar hukuntawa da kuma tsige tsohon shugaban Amurkan Donald Trump a karo na biyu bisa zargin ‘tunzura mutane’ wajen aikata laifi a majalisar dattawan.

Hakan kuwa ya biyo bayan sanarwar da Kakakin Majalisar Wakilai ta Amurkan Nancy Pelosi ta yi ne na cewa a ranar Litinin mai zuwa za ta gabatar wa majalisar dattawan da takardar buƙatar hukuntawa da kuma tsige Trump ɗin.

Yayin da yake tabbatar da hakan shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Amurkan Chuck Schumer ya ce lalle za a gudanar da shari’a a majalisar dattawan da kuma kaɗa kuri’ar ko a hukunta tsohon shugaban ko kuma a’a, yana mai cewa lalle za a yi shari’a mai cike da adalci ga tsohon shugaba Trump ɗin.

A ranar 13 ga watan Janairun nan ne, mako guda kafin shugaba Trump ɗin ya sauka daga karagar mulki ‘yan majalisar wakilan su 232 suka kaɗa kuri’ar amincewa da tsige Trump daga karagar mulki alhali wasu 197 kuma sun ƙi amincewa da hakan lamarin da ta sanya aka sanar da tsige shi ɗin a karo na biyu na mulkinsa.

‘Yan majalisar dai sun zargi Trump ne da tunzura magoya bayansa wajen kai harin da suka kai majalisar dokokin ƙasar a ranar 6 ga watan Janairu.

Masana harkokin dokoki da siyasa sun bayyana cewa duk da cewa Trump ya sauka daga mulki, amma tsige shi zai janyo masa rasa wasu muhimman abubuwa da kuma wasu damarmaki da tsohon shugaban ƙasa ke samu bugu da ƙari kan shirinsa na sake tsayawa takarar shugabancin Amurkan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!