​Iran Ta Kakaba Wa Trump Da Wasu Mukarabansa Takunkumi

2021-01-20 14:59:55
​Iran Ta Kakaba Wa Trump Da Wasu Mukarabansa Takunkumi

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta sanya wa Donald Trump, da wasu na hannun damansa takunkumi, saboda abunta ta kira aikata laifukan ta’addanci da goyan bayan ta’addancin.

Wata sanarwa, da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, ta fitar da yammacin jiya Talata, ta zayyano sunayen jami’an Amurkar da suka hada da Trump a sahun gaba, sai sakataren harkokin wajensa, Mike Pompeo, da tsohon sakataren harkokin tsaro Mark Esper, da Steven Mnuchin sakataren baitamalun Amurka, da kuam Gina Haspel darektar hukumar CIA), sai kuma tsohon mashawarcin Trump na harkokin tsaron kasa John Bolton.

Dukkan su dai Iran, ta ce ta kakaba masu takunkumi kan aikata ayyukan ta’addanci da ingizawa da goyan bayan ta’addanci, wanda babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaro a yankin dama duniya baki daya, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, ta ambato a cikin sanarwar.

Wasu laifukan da Iran din ta zargi Trump da aikatawa kanta su ne hana ta sanyan magunguna da kayan asibiti a lokacin da duniya ke fama da annobar korona.

Matakin na Iran dai na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage ‘yan sa’o’I Trump ya sauka daga shugabancin Amurka.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!