Masu Sharhi: Wasiƙar Jagora Imam Khamenei Ga Matasan Turai Ta Fahimtar Da Su Haƙiƙanin Musulunci

2021-01-19 20:32:46
Masu Sharhi: Wasiƙar Jagora Imam Khamenei Ga Matasan Turai Ta Fahimtar Da Su Haƙiƙanin Musulunci

A daidai lokacin da ake shirin tunawa da zagayowar shekarar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike da wasikarsa ta farko ga matasan Turai shekaru shida da suka gabata, masana na ci gaba da sharhi kan tasirin wasiƙar da kuma bayyana ta a matsayin abin da taimaka wajen fahimtar da matasan Turai haƙiƙanin addinin Musulunci.

A ranar 21 ga watan Janairun 2015 ne dai, biyo bayan wasu hare-haren ta’addanci da suka faru a ƙasar Faransa da kuma irin yadda wasu suka yi amfani da hakan wajen baƙanta sunan musulunci, Ayatullah Khamenei, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aike da wata wasiƙa ga matasan ƙasashen Turai da nufin janyo hankulansu kan abin da ke faruwa da kuma su fahimci haƙiƙanin addinin Musulunci daga ma’abotansa ba daga maƙiyansa waɗanda a kullum suke ƙoƙarin baƙanta sunansa ba.

A wasiƙar tasa Jagoran ya bayyana cewar yana magana da matasan ne a matsayinsu na manyan gobe, wadanda makomar al'umma da kuma kasarsu take hannunsu; sannan kuma saboda yana ganin zukatansu cike suke da neman sanin gaskiya. Kamar yadda kuma ya ce ba wai yana magana ne da ‘yan siyasa da jami'an gwamnatocin waɗannan ƙasashen ba ne don kuwa a cewarsa: “Na yi amanna da cewa da gangan sannan kuma da saninsu suka kawar da siyasarsu daga tafarkin gaskiya da haƙiƙa.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Magana ta da ku kan Musulunci ne, musamman ma dangane irin abin da ake gabatar muku da shi a matsayin Musuluncin” da aka mayar da shi wani “gagarumin abin tsoro”.

Daga nan sai Jagoran ya kirayi matasan da kada su bari a yi wasa da hankulansu da kuma katange su daga haƙiƙanin koyarwar musulunci, su ba da himma da ƙoƙari wajen binciken haƙiƙanin koyarwar Musulunci musamman a wannan zamani da duniya ta zamanto tamkar gari guda.

Don haka Jagoran ya kirayi matasan da cewa: “Kada ku bari wannan dama ta fahimtar gaskiyar Musulunci ta kubuce muku, don me yiyuwa ta hanyar wannan jin nauyi a jika da kuke da shi, al'ummomi masu zuwa za su rubuta tarihin irin wannan mu'amala da kasashen yammaci suka yi da Musulunci cikin sauki ba tare da wahala ba”.

Har ila yau a ƙarshen shekara ta 2015 ɗin ma a watan Nuwamba, Jagoran ya sake rubuta wata wasiƙar ga matasan Turan don ƙara fayyace musu wasu batutuwan na daban dangane da addinin Musulunci, biyo bayan ci gaba da ƙoƙarin baƙanta sunan Musuluncin da maƙiyan suke yi.

Ga cikakkiyar wasikar:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai


Zuwa Ga Dukkanin Matasan Kasashen Turai Da Arewacin Amurka


Lamurrann baya-bayan nan da suka faru a kasar Faransa da makamantansu a wasu kasashen Yammaci, su ne suka sanya ni ganin ya dace in yi magana da ku kai tsaye. Ina magana da ku ne, Ya ku matasa; ba wai saboda na raina iyayenku ba, face dai sai saboda ku ne manyan gobe, wadanda makomar al'umma da kuma kasarku take hannunsu; sannan kuma saboda ina ganin zukatanku cike suke da neman sanin gaskiya. Haka nan kuma ba wai ina magana ne da ‘yan siyasa da jami'an gwamnatocinku ba ne, don kuwa na yi amanna da cewa da gangan sannan kuma da saninsu suka kawar da siyasarsu daga tafarkin gaskiya da hakika.


Magana ta da ku kan Musulunci ne, musamman ma dangane irin abin da ake gabatar muku da shi a matsayin Musuluncin.

Tsawon shekaru ashirin din da suka gabata zuwa sama - wato tun daga lokacin rugujewar Tarayyar Sobiyeti - an gudanar da gagarumin kokarin bayyanar da wannan addini mai girma a matsayin wani gagarumin abin tsoro. Abin bakin cikin shi ne cewa irin wannan yanayi na sanya tsoro da kyamar (wannan addini) wani lamari ne mai tsoron tarihi cikin tarihin siyasar kasashen yammaci. Ni dai a nan ba ina so ne in yi magana dangane da ‘irin kyama da tsoratarwa' daban-daban da ya zuwa yanzu aka sanya cikin zukatan al'ummomin kasashen yammaci ba. Idan kuka koma kadan cikin tarihi, za ku ga cewa sabbin marubuta tarihi, sun soki mu'amalar rashin adalci da gaskiya da gwamnatocin yammaci suka yi wa al'ummomi da al'adun duniya. Tarihin Turai da Amurka ya rusunar da kansa cikin kunya saboda bautar da mutane, mulkin mallaka da kuma zaluntar wadanda ba fararen fata da kuma wadanda ba Kiristoci ba da suka yi. Masana da malaman tarihinku suna cikin kunyar irin zubar da jinin da aka yi da sunan addini tsakanin mabiya darikar Katolika da Protestant ko kuma da sunan ‘yan kasanci da kabilanci a yakukuwan duniya na daya da na biyu. Shi kansa hakan wani abin jinjinawa ne.


Manufar bijiro da wani bangare na wannan doguwar fehrisa na abubuwan da suka faru, ba ita ce sukar tarihi ba, face dai abin da nake so shi ne ku tambayi masananku shin me ya sa a koda yaushe sai bayan jinkiri na gomomin shekaru ko kuma ma daruruwan shekaru ne lamirin al'ummomin yammaci ya ke farkawa da kuma dawowa cikin hayacinsa? Me ya sa ake damfara lamirin mutane ga abubuwan da suka faru cikin tarihin shekaru aru aru ba batutuwan da suke faruwa a halin yanzu ba? Me ya sa ake kange mutane daga fahimtar lamurra masu muhimmanci irin su hanyoyin mu'amala da al'adu da kuma tunani na Musulunci?

Ku da kanku kun san cewa wulakanci da haifar da kiyayya da kirkirar tsoron sauran mutane na boge, suna a matsayin wani fage ne da aka yi tarayya cikinsa wajen haifar da dukkanin irin wadannan zalunci da mummunan amfani da mutane. A halin yanzu ina son tambayarku, shin me ya sa yanzu aka dawo da tsohuwar siyasar sanya tsoro da kyamar Musulunci da musulmi? Me ya sa tsarin mulki na duniya a halin yanzu ya sanya tunani na Musulunci a gaba? Shin wasu abubuwa ne da suke cikin tunani da koyarwar Musulunci da har zai zamanto kafar ungulu ga tsare-tsare da siyasar manyan kasashen duniya, sannan kuma me za su samu wajen bakanta fuskar Musulunci?


A saboda haka, bukata ta ta farko ita ce ku yi tambaya da kuma binciko dalilin irin wannan gagarumin kokari na bata sunan Musulunci. Bukata ta ta biyu, ita ce yayin mayar da martani ga irin wannan gagarumin bakar farfagandar bata sunan Musulunci (da ake yi), ku yi kokarin fahimtar wannan addini (Musulunci) da koyarwar ta hakika kai tsaye. Lafiyayyen hankali yana hukumta wajibcin sanin hakikanin abin da ake tsoratar da ku shi da kuma nesanta ku daga gare shi. Ni dai ba ina cewa ne lalle sai kun yarda da fahimta ta ko fahimtar wani kan Musulunci ba, sai dai abin da nake cewa shi ne kada ku bari a kange ku daga wannan hakikar wacce take da tasiri cikin duniyar yau saboda cimma wata bakar manufa. Kada ku bari cikin riya su gabatar muku da ‘yan ta'addan da suke karkashin ikonsu a matsayin wakilan Musulunci. Kamata yayi ku fahimci Musulunci daga tushensa na asali. Ku fahimci Musulunci ta hanyar Alkur'ani da rayuwar Annabin Musulunci (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa). A nan ina son in tambaye ku, shin ya zuwa yanzu kun taba karanta Alkur'anin musulmi kai tsaye? Shin kun taba karantar koyarwar Annabin Musulunci (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayensa) da kyawawan halaye da ‘yan'adamtakarsa? Shin ya zuwa yanzu kun fahimci sakon Musulunci ta wata kafa ta daban, ba kafar watsa labarai ba? Shin kun taba tambayar kanku ya ya aka yi wannan Musuluncin, sannan bisa wasu koyarwa ya samu daman zama mafi girman al'adu da ci gaban ilimi da tunani na duniya sannan kuma ya tarbiyyantar da mafi girma da kyawun masana da masu tunani na duniya?

Ina kiranku da kada ku bari a yi amfani da bakar siyasa da wauta wajen katange ku daga gaskiya, da kuma kawar da yiyuwar yin alkalanci cikin adalci daga gare ku. A halin yanzu da kafafen sadarwa suka rusa ganuwar kan iyakokin kasashe, kada ku bari a kange ku cikin kirkirarrun kan iyakoki na boge. Duk da cewa babu wani mutum, a kan kansa, da zai cike wannan gibin da aka samar, amma kowane guda daga cikinku zai iya samar da gadar tunani da adalci a kan wannan gibin da aka haifar. Duk da cewa wannan kalubalen da aka kirkira tsakanin Musulunci da ku matasa wani kalubale ne mai sarkakiyar gaske, to amma hakan yana iya kirkiro sabbin tambayoyi cikin zukatanku da suke neman sanin hakika. Kokari wajen samo amsoshin wadannan tambayoyi, zai samar muku da wata dama ta gano wasu sabbin gaskiyar.


A saboda haka, kada ku bari wannan dama ta fahimtar gaskiyar Musulunci ta kubuce muku, don me yiyuwa ta hanyar wannan jin nauyi a jika da kuke da shi, al'ummomi masu zuwa za su rubuta tarihin irin wannan mu'amala da kasashen yammaci suka yi da Musulunci cikin sauki ba tare da wahala ba.


Sayyid Ali Khamenei

1/11/1393

21/01/2015


Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!