Uganda Ta Yi Tir Da Ƙoƙarin Amurka Na Tsoma Baki Cikin Harkokin Cikin Gidan Ƙasar

2021-01-19 20:07:45
Uganda Ta Yi Tir Da Ƙoƙarin Amurka Na Tsoma Baki Cikin Harkokin Cikin Gidan Ƙasar

Gwamnatin ƙasar Uganda ta zargi Amurka da ƙoƙarin tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta da kuma ƙoƙari wajen dagula sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a makon da ya wuce, bayan da jakadiyar Amurka a ƙasar Ugandan yayi ƙoƙarin ganawa da madugun ‘yan adawa na ƙasar da aka masa ɗaurin talala a gidansa.

Kakakin gwamnatin Ugandan Ofwono Opondo ne ya bayyana hakan a yau ɗin nan Talata inda ya ce abin da jakadiyar Amurka a Ugandan Natalie Brown take ƙoƙarin yi tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan ƙasar Uganda musamman abin da ya shafi zaɓe, inda take ƙoƙarin dagula sakamakon zaɓen da kuma abin da mutane suka zaɓa.

Kakakin gwamnatin ya ce bai kamata jakadiyar ta yi wani abu da ya saɓa wa al’adar aikin diplomasiyya ba yana mai cewa Jakadiyar tana da tsohon tarihi na haifar da rikici a dukkanin ƙasashen da ta yi aiki a can, don haka ya ce mata ta kwana da shirin cewa lalle a wannan karonkan gwamnatin Ugandan tana zuba mata ido.

Hakan dai yana zuwa ne bayan da mahukuntan Ugandan suka hada Mrs. Brown tafiya don ganawa da madugun ‘yan tawayen wanda kuma ya sha kaye a zaben shugaban ƙasar da aka gudanar wato Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine a gidansa da ke wajen birnin Kampala.

Ofishin jakadancin Amurkan dai, cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce Jakadiyar tana so ne ta gana da Bobi Wine ɗin don abin da ya kira ‘tabbatar da lafiyarsa’ lamarin da gwamnatin Ugandan ta hana tana mai cewa Amurkan tana ƙoƙarin haifar da fitina ne a ƙasar.

Ofisoshin jakadancin Amurka a ƙasashe daban-daban sun kasance wani sansani na haifar da fitina da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan waɗannan ƙasashen musamman a lokacin gudanar da zaɓuɓɓuka a waɗannan ƙasashen.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!