Pfizer : Kafofin Watsa Labaran Yamma Sun Yi Gum Kan Mutuwar Mutane

2021-01-18 14:55:20
Pfizer : Kafofin Watsa Labaran Yamma Sun Yi Gum Kan Mutuwar Mutane

A ranar 14 ga wata, wasu tsofaffi 23 ‘yan kasar Norway, sun mutu bayan an yi musu allurar rigakafin cutar COVID-19 da kamfanin Pfizer na Amurka ya hada.

Kuma hukumar binciken magunguna ta kasar, ta gaskata cewa, tsofaffi 13 daga cikinsu, sun mutu ne sakamakon illar allurar rigakafin COVID-19 da aka yi musu.

Ya zuwa yanzu, gaba daya akwai mutane dubu 25 da aka yi wa allurar rigakafin cutar COVID-19 a kasar Norway, kuma cikinsu, mutane 23 sun rasu bayan an yi musu allurar.

A sa’i daya kuma, akwai ‘yan kasar Jamus 10 da suka mutu bayan karbar allurar rigakafin COVID-19 da kamfanin Pfizer ya samar, yayin da mutum daya a kasar Faransa ya mutu.

Amma abin mamaki shi ne, dukkan kafofin watsa labarai na kasashen yamma sun yi shiru kan wannan batu.

Dangane da wannan, dan majalisar dokokin kasar Rasha Mr. Zhuravlev ya bayyana cewa, wannan shi ne mugun sakamakon da yakin kasuwanci tsakanin kamfanonin hada magunguna na kasashen yamma ya haddasa, inda ya ce, wadannan kasashe suna gwaji kan mutane ta hanyar yi musu allurar rigakafin cutar COVID-19.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!