Uganda: An Fara Gudanar Da Zaɓen Shugaban Kasa

Rahotanni daga ƙasar Uganda sun bayyana cewar ana ci gaba da kaɗa kuri’a a zaɓen shugaban ƙasa mafi ɗaukar hankula a ƙasar inda shugaba mai ci Yoweri Museveni ya ke takara da ‘yan takara 10 sai dai mafi ficen cikinsu shi ne mawaƙin nan da ya zama ɗan siyasa da aka fi sani da Bobi Wine.
Zaɓen na bana dai ya fuskanci mafi munin tashin hankali tsawon tarihin zaɓuɓɓuka na baya-bayan nan a ƙasar inda ake zargin cewa jami’an tsaron ƙasar sun kashe sama da mutane 50 biyo bayan diran mikiyan da suke yi wa ‘yan’adawa da kuma ci gaba da kamu da tsare jagororin ‘yan adawan.
Jami’an tsaron dai sun ce sun ɗau waɗannan matakai na
takura wa jama’a ɗin ne
saboda tabbatar da an bi dokokin kiwon lafiya don faɗa da cutar nan ta
COVID-19.
Rahotanni da suke fitowa
daga ƙasar suna nuni da cewa an fara kaɗa
kuri’ar a mazaɓu da dama a duk faɗin
ƙasar duk kuwa da ƙorafin da wasu suke yi
na jinkiri wajen fara kaɗa kuri’ar sakamakon jinkirin isowar kayayyakin aikin.
Wannan dai shi ne karo na
shida da shugaba Museveni, wanda yake kan karagar mulkin ƙasar Ugandan
tun 1986, ya ke takarar shugabancin ƙasar, inda a wannan karon yana takarane
da wasu ‘yan takara 10, sai dai babbar
kalubalen da yake fuskanta tana fitowane daga Bobi Wine, matashi ɗan shekaru 38
a duniya wanda kuma yake da goyon baya sosai daga wajen matasan ƙasar.
Mahukutan dai sun ce kimanin mutane miliyan 18 ne suka yi rajistar
sunayensu don kaɗa kuri’a a zaɓen na
yau, sannan kuma wajibi ne ɗan takara ya samu sama da kashi 50 cikin ɗari na
kuri’un da aka kaɗa ɗin don guje wa tafiya zuwa zagaye na biyu.
Ana sa ran za a fitar da
sakamakon zaɓen ne sa’oi 48 bayan gama zaɓen na shugaban ƙasa wanda ake yinsa
tare da na ‘yan majalisu.
Ana zargin gwamnatin ƙasar da tursasawa ‘yan adawa da kuma rufe hanyoyin sadarwa musamman na zamani a ƙasar lamarin da gwamnatin tace ta yi hakan ne don tabbatar da tsaron ƙasar.