Majalisar Wakilan Amurka Ta Tsige Trump Daga Shugabancin Amurka A Karo Na Biyu

2021-01-14 09:18:39
Majalisar Wakilan Amurka Ta Tsige Trump Daga Shugabancin Amurka A Karo Na Biyu

Majalisar wakilan Amurka ta tsige shugaban ƙasar Donald Trump saboda samunsa da laifin tunzura maboya bayansa da ya kai su ga kai hari majalisar ƙasar a makon da ya wuce, wanda hakan ya sanya shi zama shugaban Amurka na farko da aka tsige shi sau biyu a tarihin Amurkan.

A daren jiya ne dai ‘yan majalisar suka kaɗa kuri’ar tsige shugaba Trump bayan wata muhawara mai zafi da suka gudanar kan wannan batun inda daga ƙarshe dai suka kaɗa kuri’ar amincewa da tsigewar da ‘yan majalisar daga jam’iyyar Democrats suka gabatar mako guda kafin wa’adin mulkinsa ya ƙare.

Sakamakon kuri’ar da aka kaɗa ɗin dai yana nuni da cewa ‘yan majalisar 232 sun amincewa da tsigewa alhali waɗanda ba su amince ɗin ba su 197 ne.

Majalisar dai wacce ‘yan Democrats suke da rinjaye a cikinta ta zargi Mr. Trump ne da tunzura magoya bayansa su kai hari majalisar dokokin ƙasar a ranar Larabar makon da ya wuce a daidai lokacin da ‘yan majalisar suke shirin tabbatar da zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a watan Nuwamban bara wanda ɗan takaran jam’iyyar Democrats Joe Biden ya lashe. Trump ɗin ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen dai yana zargin an tafka maguɗi zargin da dukkanin cibiyoyin da ke kula da zaɓe a ƙasar suka yi watsi da shi.

Tsige Trump ɗin da aka yi a majalisar wakilan dai zai kai ga yi masa shari’a a majalisar dattijan Amurkan, inda ake buƙatar amincewar kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar wajen tabbatar da laifinsa, lamarin da ake ganin cewa da wuya a gudanar da shi kafin wa’adin mulkin nasa ya ƙare a ranar 20 ga watan Janairun nan.

Ana ganin za a gudanar da wannan shari’ar ce bayan ma ya sauka daga karagar mulkin, wanda idan har aka same shi da laifi to za a iya haramta masa sake riƙe duk wani muƙami na gwamnati kuma a Amurkan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!