Rabin Jama'ar Faransa Na Adawa Da Kasancewar Sojojin Kasar A Mali

2021-01-12 21:35:52
Rabin Jama'ar Faransa Na Adawa Da Kasancewar Sojojin Kasar A Mali

Wani rahoto na jin ra’ayin jama’a da aka fitar a faransa ya nuna cewa rabin ‘yan kasar na nuna adawa da kasancewar sojojin Faransar a kasar Mali.

Rahoron wanda cibiyar bincike da jin ra’ayin jama’a ta Ifop a faransar ta gudanar shi ne irinsa na farko da aka gudanar tun bayan da sojojin na faransa suka sanya kafa a kasar Mali da nufin yaki da masu tsatsauran ra’ayi a cikin shekara 2013, kamar yadda mujallar Le Point, ta rawaito.

Binciken ya nuna cewa sama da faransawa kashi 51%, ne basa bukatar kasancewar tawagar ta Barkhane a Mali, yayin da kashi 19% ne kawai suka gamsu da jibge dakarun faransar a yankin na Sahel da ya hada kasashen (Mali, Nijar, Burkina Faso, Chadi, da Mauritania).

A shekara 2013, bayan yantar da birnin Tombouctou, faransawa kashi 73% ne suka goyi bayan kasancewar sojojin a Mali, amma a karshen shekara 2019 bayan mutuwar sojojin faransa 13, goyan bayan kasancewar sojojin daga faransawa ya ragu zuwa kashi 58 cikin dari.

A baya bayan nan dai sojojin faransa 5 ne suka mutu a Mali, wanda ya sanya jimmilar sojojin faransa da suka mutu a yankin sahel ya kai 50.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!