Dakarun Iran Na Shirin Fara Wani Gagarimin Atisaye

2021-01-10 21:16:17
Dakarun Iran Na Shirin Fara Wani Gagarimin Atisaye

Kwamadan dakarun sojin kasa na Iran, ya sanar da cewa kasar na shirin fara wani gagarimin atisaye a cikin kwanaki masu.

Da yake sanar da hakan a wata hira da kamfanin dilancin labaren kasar na IRNA, Birigediya Janar Kiomars Heydari, ya ce atisayen za’a gudanar da shi nan kusa, a yankin kudu maso gabashin kasar ta Iran.

Za’a kuma yi amfani da duk ire iren makamman da Iran take dasu, tare da sauren bataliyar sojojin kasar a fannoni daban daban.

Birigediya Janar Heydari, ya kara da cewa atisayen umarni ne na jagoran juyin juya halin musulinci na kasar, saboda take taken makiya a yankin.

Za’a kuma gudanar da atisayen a iyakokin kasar, saboda su ne jan layi a game da batun tabbatar da tsaro a kasar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!