Hashd Al-Shaabi: Takunkumin Amurka A Kan Babban Kwamandanmu Abin Alfahari Ne

Dakarun sa kai na al’ummar Iraki
Hashd Al-shaabi sun mayar da kakkausan martani kan takunkuman da Amurka ta
sanar da cewa ta kakaba wa babban kwamandansu Faleh Fayyad.
A cikin wani bayani wanda bangaren
yada labarai na rundunar Hashd Al-shaabi
ya fitar, ya bayyana takunkumin Amurka a kan Faleh Fayyad da cewa abin alfahari
ne a gare shi da ma dukkanin dakarun Hashd Al-shaabi.
Bayanin ya ce, wannan matakin da
gwamnatin Amurka ta dauka a kan mutumin da ya kasance a sahun gaba wajen yakar ‘yan
ta’addan Daesh a Iraki, tare da fatattakarsu da karya lagonsu, ya kara fito da
komai a fili kan cewa, Amurka da Daesh da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda masu
da’awar jihadi duk abu daya ne, domin kuwa babbar manufarsu ita ce rusa
kasashen musulmi da kuma bata sunan addinin muslunci a idon duniya.
A jiya ne gwamnatin Trump ta sanar
da cewa ta saka babban kwamandan dakarun Hashd Al-shaabi na kasar Iraki Faleh
Fayyad a cikin jerin wadanda ta kakaba wa takunkumi.
Tun kafin wannan lokacin dai Fayyad
ya tsaya kai da fata akan cewa dole ne
Amurka ta fitar da dukkanin sojojinta da suka rage a cikin Iraki, bayan da
majalisar dokokin kasar ta fitar da wani kudiri kan hakan, inda ya jaddada cewa
rashin ficewar dakarun Amurka daga Iraki, yana a matsayin tozarta majalisar
dokokin kasar ne wadda take wakiltar dukkanin al’ummar Iraki.
015