Shugabannin Duniya Na Ci Gaba Da Tir Da Tarzomar Da Trump Da Magoya Bayansa Suka Tayar

Shugabannin kasashen duniya daban-daban na ci gaba da yin Allah wadai da tarzomar da shugaban Amurka Trump da magoya bayansa suka tayar a majalisar dokokin Amurka don hana tabbatar da Joe Biden a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban Amurka a shekaran jiya Laraba.
Shugaban baya-bayan nan da ya yi wannan
Allah wadan shi ne shugaban ƙasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa wanda cikin wani
saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya bayyana cewar: Abin da ke faruwa a
Amurka yana nuni da cewa daga yanzu Amurka ba ta da haƙƙin sake sanya wa wata
ƙasa takunkumi saboda fakewa da batun demokraɗiyya.
Kafin hakan ma dai shugabannin ƙasashen
Turai da dama sun nuna damuwarsu da abin da ya faru a Amurkan.
Firayi ministan Birtaniyya Borris
Johnson ya bayyana abin da ya faru a Amurka a matsayin abin kunya yana mai
shaguɓe wa shugaba Trump din da cewa kamata yayi a miƙa mulki cikin lumana da
tsari.
Ita ma
shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ta ji matuƙar taƙaici ganin yadda
lamurra suka kasance a Amurka, kamar yadda shi ma firayi ministan Indiya
Narendra Modi ya ce wajibi ne Trump ɗin ya bari a miƙa mulki cikin lumana yana
mai cewa: "Ba zai yiwu a lalata
dimkokraɗiyya ba ta hanyar gudanar da zanga-zanga ba bisa ƙa'ida ba," in
ji shi.
Su ma a nasu ɓangaren tsoffin shugabannin Amurkan Barack
Obama da Bill Clinton sun zargi shugaba Trump da haifar da wannan tarzoma da
tashin tashina a ƙasar suna mai kiransa da magoya bayan nasa da su amince da
haƙiƙa.
A shekaran jiya ne dai magoya bayan shugaba Trump, sakamakon tunzura su da yayi, suka mamaye majalisar dokokin Amurka don hana tabbatar da sakamakon zaɓen shugaban Amurkan da aka gudanar wanda ɗan takarar jam’iyyar Democrats Joe Biden ya lashe.