​Iran:Kwace Kudaden Iran Dalar Amurka Miliyon $7 Wanda Amurka Tayi Wani Naau’in Fashi Ne

2021-01-06 22:45:26
​Iran:Kwace Kudaden Iran Dalar Amurka Miliyon $7 Wanda Amurka Tayi Wani Naau’in Fashi Ne

Gwamnatin kasar Iran ta bayyana kwace kadarorin kasar da suke kasashen waje wanda gwamnatin wacce wa’adinta ke karewa ta ke yi wani nau’in fashi da makamani. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya Talata ce, ma’aikatar kudin kasar Amurka ta bada sanarwan kwace dalar Amurka miliyon 7 na kasar Iran, a matsayin kudaden diyya ga barnan da wasu, wadanda ta kira ‘yan ta’adda suka yi na kaucewa takunkuman tattalin arzikin da Amurkan ta dorawa kasar.

Wannan bas hi ne karon farko wanda gwamnatin Donal Trump take kwace biliyoyin dalar Amurka na kadarorin kasar Iran wadanda Amurkan ta hana a taba a bankunan kasashen duniya ba.

Labarin ya nakalto David Burns mataimakin Antoni Janar na kasar Amurka yana cewa an kwace wadanan kudade ne don Iran tana kokarin isar da su hannun wasu yan ta’adda wadanda zasu karya takunkuman da Amurka ta dorawa kasar.

Kafin haka dai a cikin watan Maris na shekara ta 2017 Amurka ta kwace dalar Amurka biliyon 1.4 mallakin kasar Iran, don abinda da kira diya ga iyalan wane ba Amurke ma’aikacin FBI wanda ya bace a kasar Iran a shekara ta 2007.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!