Ana Ci Gaba Da Wasannin Sada Zumunta Na Kasashen Afirka 4 A Kasar Kamaru

2021-01-03 19:20:10
Ana Ci Gaba Da Wasannin Sada Zumunta Na Kasashen Afirka 4 A Kasar Kamaru

Wasan kwallon kafar na sada zumunta ya kunshi kasashen Uganda, Niger, Zambia da kuma ita kanta kasar ta Kamaru mai masaukin baki.

Kasar Zambia ta fara da shige wa gaba akan ‘yan wasan jamhuriyar Nijar, inda dan was Collins Sikombe ya zura kwallon farko a miniti na 6 da fara wasan.

Cin kwallo na biyu da dan wasan Zambia mai suna Zanaco ya yi ya kasance a adaidai mituna 59 daga bude wasan, sai kuma Moses Phiri a tsakanin minti na 37.

Su kuwa yan wasan jamhuriyar Nijar sun ci kwallnsu ta farko ne ta hannun Jibrilla Issa a minti na 13, sannan kuma ya sake cin wata kallon ta biyu a daidai miniti na 67.

Isa Amadu ya ya ci kwallo a daidai minti na 79, da hakan ya bai wa kasashen biyu maki daidaya a ranar farko ta bude wasannin.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!