Chadi:A Karon Farko An Kafa Dokar Hana Fita A Babban Birnin Kasar Saboda Dakile Yaduwar Cutar Korona

2021-01-02 20:14:31
Chadi:A Karon Farko An Kafa Dokar Hana Fita A Babban Birnin Kasar Saboda Dakile Yaduwar Cutar Korona

Gwamnatin kasar Chadi ta kafa dokar hana fita, na dare da rana a babban birnin kasar wato N’DJAMENA a jiya daya da watan Jenerun shekara ta 2021.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce shugaban kasar ta Chadi Idriss Deby ne ya kafa dokar a jiya Jumma’a. Dokar ta hana taron mutane fiye da 10, sannan ta hana fita daga gidaje na tsawon mako guda, sai don lalura.

Kasar chadi dai tana cikin kasashen da cutar korona bata yadu sosaiba a yankin yammacin Afirka. Labarin ya kara da cewa tun lokacin bullar cutar a ckin watan Maris na shekarar da ta gabata, mutane 2,113 ne kacal suka kamu da cutar a kasar, zuwa karshen shekarar. Sannan mutane 104 ne suka rasa rayukansu.

Labarin ya ce akwai yiyuwan a tsawaitata dokar hana fitan idan akwai bukatar hakan. Har’ila yau dokar zata shafi sauka da tashin jiragen sama in banda jiragen daukar kaya, wato Cargo.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!