Aljeriya Za Ta Sayi Riga Kafin Korona Spoutnik V, Na Rasha

2020-12-31 21:50:00
Aljeriya Za Ta Sayi Riga Kafin Korona Spoutnik V, Na Rasha

Gwamnatin Aljeriya ta sanar da cewa za ta karbi riga kafin cutar korona na kasar Rasha Spoutnik V, domin yi wa jama’arta riga kafin cutar, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar ya sanar.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Aljeriyar ta sanar da cimma yarjejeniyar fahimtar juna da kasar Rasha domin sayen riga kafin na Spoutnik V, domin fara yi wa ‘yan kasar riga kafin cutar a cikin watan Janairu.

A cewar kafofin yada labarai daga Aljeriya, riga kafin da Rasha ta samar, bai da matsaloli wajen jigilarsa, da kuma farashi.

Aljeriya dai ta ce ta ware kudade kimanin miliyan 10 na Euro domin sayen riga kafin na Sputnik dubu 500, wanda masana magunguna a Rasha suka bayyana cewa yana da inganci a sama da kashi casa’in cikin dari.

A ranar 13 ga watan Disamba ne, shugaban kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune, ya baiwa gwamnatin kasar ta gaggauta sayen riga kafin na Rasha domin fara yi wa ‘yan kasar riga kafi a watan Janairu.

Alkalumman da hukumomin Aljeriya suka fitar sun nuna cewa mutane kimanin dubu dari ne suka kamu da cutar, sannan 2,750 suka rasa rayukansu sakamakon cutar.

Shugaban kasar ma yana daga cikin wadanda suka kamu inda ya shafe tsawon lokaci ya na jinyar cutar a kasar Jamus.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!