Rundunar Sojojin Sama A Nigeria Ta Sayo Sabbin Jiragen Yaki

2020-12-29 11:03:25
Rundunar Sojojin Sama A Nigeria Ta Sayo Sabbin Jiragen Yaki

Bisa la’akari da yadda yanayin tsaro ya kara tabarbarewa a Fadin Nigeria musamman a Arewacin kasar, rundunar sojin sama ta Nigeria NAF ta sayo sabbin jiragen yaki domin tunkarar wannan matsala da ta dade tana ci wa alumma tuwo a kwarya, inda ta sayo jiragen yaki masu saukar Ungulu kirar MI 171 E da kuma Karin wani babban Jet.

A nasa bangaren shugaban rundunar sojojin sama ta Nigeria Air Mashall Sadiku Abubukar ya ce yanzu haka dai jiragen yakin sun kwashe sa’o’i da yawa suna shawagi a sama a Arewa masu gabashin Nigeria. Baya ga wadannan sabbin akwai wasu jiragen yaki guda 23 da ake musu gyara domin ci gaba da amfani da su.

Ya kara da cewa idan za’a tuna a shekara ta 2015 kashi 35 cikin 100 na jiragen yakin Nigeria ne kawai ke tashi , amma yanzu kusan kimanin 85 cikin dari ne ke tashi kuma suna aiki sosai kamar yadda ya kamata , wanda hakan yana kara karfin guiwa a kokarin da gwamnati ke yi na ganin an kawo karshen yan ta’adda da kuma yan kungiyar boko Haram.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!