Nijar: An Fara Kada Kuri'a A Zaben Shugaban Kasa Da Na 'Yan Majalisar Dokoki

2020-12-27 14:48:40
 Nijar: An Fara Kada Kuri'a A Zaben Shugaban Kasa Da Na 'Yan Majalisar Dokoki

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambaci cewa tuni aka fara kada kuri’u a sassan kasar daban-daban.

Shugaban kasar mai ci Muhammadu Issufou zai sauka daga kan karagar mulki bayan karewar wa’adinsa na shekaru 10.

Jami’iyyarsa ta PNDS tarayya ta tsayar da Muhammad Bazoum a matsayin wanda zai maye gurbin shugaba Issoufu idan har sun ci zabe.

A tsawon lokacin yakin neman zabe, babu wani rahoto na tashe-tashen hankula.

Da akwai mutane miliyan bakwai da kusan rabi da su ka cancanci yin zabe.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!