​Najeriya: NMA Ta Ce Likitoci 20 Sun Mutu A Wannan Mako Sakamakon Cututtuka Masu Alaka Da Corona

2020-12-26 19:10:42
​Najeriya: NMA Ta Ce Likitoci 20 Sun Mutu A Wannan Mako Sakamakon Cututtuka Masu Alaka Da Corona

Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya NMA ya bayyana cewa likitoci 20 suka mutu a wannan makon sanadiyyar cututtuka masu alaka da Corona.

Enema Amodu ya bayyana hakan ne a jiya a wani taron manema labarai, inda ya ce wadanda suka mutu din sun hada da jami’an lafiya da na tuntuba da wasu farfesoshi da tantagaryar likitoci.

“ Mu da ke aikin harkokin kula da lafiya, mun rasa abokan aikin mu da dama. Wadanda korona ta kashe a cikin mako daya kadai a fadin kasar nan, sun kai likitoci 20.”

Hukumar Kula da Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO), ta ce zuwa Yulin da ya gabata sama da jami’an kula da lafiya 10,000 ne suka kamu da cutar korona a fadin Afrika.

Sai dai zuwa yanzu ba za a ma iya tantance adadin yawan jam’an kiwon lafiyar da suka kamu a Najeriya ba.

Amodu ya yi gargadin a tashi tsaye wajen kare kai daga kamuwa da cutar, domin a cewarsa a yanzu korona da ta sake dawowa, ta fi ta baya karfi da saurin kassara mutane.

Tun bayan bullar sabuwar corona a kasar Burtaniya, kasashe da dama suke daukar matakai domin ganin sun kauce wa bullarta a cikin kasashensu.

A baya-bayan an yi ta yada cewa sabuwar cutar da ta sake bulla a Burtaniya, an ga alamunta a cikin Najeriya, duk kuwa da cewa hukumomin kiwon lafiya na Najeriya suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!