Kungiyar Boko Haram A Nigeria Ta Kashe Mutane Da Dama Da Kuma Kona Wata Majami’a A Arewa Maso Gabashin Kasar

2020-12-25 20:07:20
 Kungiyar Boko Haram A Nigeria Ta Kashe Mutane  Da Dama Da Kuma Kona Wata Majami’a A Arewa Maso Gabashin Kasar

A jiya Alhamsi ne dai ‘yan kungiyar ta boko haram su ka kai hari a kauyen Pem dake jihar Borno, tare da kona wata majami’a da kuma yin awon gaba da wani limamin kirista.

Wani mayakin sa-kai a yankin mai suna Abwaku Kabu ya shaidawa manema labaru cewa; ‘yan boko haram din sun kutsa cikin garin ne a jiya Alhamis da dare, inda su ka fara harbe-harben kai mai’uwa da wabi.

Kabu ya kara da cewa; A kalla mutane 7 ne maharan na boko haram su ka kashe, sannan kuma suka kone gidaje 10. Har ila yau ya ce maharan sun yi awon gaba da malamin addinin kirista bayan da suka kone wata majami’a. Kuma sun sace magungunan dake cikin dakin shan maganin kauyen, sannan su ka cinnawa gininsa wuta.

Wannan harin na kungiyar ta Bokoharam ya zo ne dai sa’oi kadan bayan da hukumar ‘yan sandan ciki ta kasar ( DSS) ta sanar da cewa; Da akwai yiyuwar akai harin ta’addanci a daidai lokacin bukukuwan Kirsimeti na mabiya addinin kirista.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!