​Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Yin Afuwa Ga Amurkawan Da Suka Yi Kisan Kai A Iraki

2020-12-24 14:24:25
​Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tir Yin Afuwa Ga Amurkawan Da Suka Yi Kisan Kai A Iraki

Majalisar Dinkin Duniya ta caccaki shugaban Amurka Donald Trump kan yafe wa ma'aikatan kamfanin tsaro na Black Water da aka same su da laifukan cin zarafi da kisan fararen hula a kasar Iraki.

Kakakin kwamitin kare hakkin bil adama a majlaisar dinkin duniya Marta Hurtado ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da matakin da bayyana matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na yafe wa Amurkawa ma’aikatan kamfanin tsaro na Black Water da suka yi kisan gilla akan fararen hula a Iraki.

Marta Hurtado ta ce abin da Trump ya yi yana a matsayin karfafa gwiwar masu aikata irin wadannan laifuka, tare da basu tabbacin cewa za su kubuta daga shari’a, wanda kuma hakan yana a mtsayin keta hurumi ne na doka, kasantuwar cewa mutanen duk an yanke musu hukunci bisa ga munanan laifukan da suka aikata na kisan gilla a kan faraen hula a Iraki.

015


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!