Laliga: Iker Casillas Ya Koma Real Madrid

Tsohon mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid,
Iker Casillas ya koma kungiyar da aiki inda aka bayyana cewa zai soma aiki da
gidauniyar dake dauke da sunan kungiyar ta Real Madrid.
Tsohon
mai tsaron ragar kungiyar Real Madrid din, Iker Casilas ya taba lashe kofuna 19
da wannan kungiya a matsayin dan wasa ciki har da gasar cin kofin zakarun turai
da La liga da sauran kofunan da ya taimakawa kungiyar ta lashe.
Wannan
gidauniya na tallata matasa tare da basu horo da ya dace a fanin kwallon kafa
kuma Iker Casilas da ya haska da kungiyar kasar Spain sau 167 tare da lashe kofin
Duniya da kungiyar Spain a shekara ta 2010 da kofin Turai a shekara ta 2008 da
2012 .
Tsohon dan wasan mai tsaron bayan ya dawo kungiyar ne bayan
share shekaru biyar da ficewa daga Real Madrid zuwa kungiyar kwallon kafa ta FC
Porto, kungiyar da a rayuwarsa ya taba wakilta banda Real Madrid.
Da
zuwan Casillas mai horar da kungiyar Real Madrid, Zinedine Zidane
yai masa barka da zuwa a lokacin da yake ganawa da manema labarai kuma Zidane,
wanda ya buga wasa da tsohon mai tsaron ragar a Real Madrid, ya shaida wa
manema labarai cewa Iker Casilas ba karamin dan wasa ba ne kuma yana mai
bayyana fatan sa na ci gaba da aiki da shi, da hurumin zai ci gaba da kawo ta
sa fahimta da sani don ci gaban kungiyar ta Real Madrid.