Habasha Ta Harba Tauraron Dan-Adam Na Biyu

2020-12-24 10:37:41
Habasha Ta Harba Tauraron Dan-Adam Na Biyu

Kasar Habasha ta yi nasarar harba tauraron dan-Adam dinta na biyu, tare da taimakon kasar Sin.

Da yake karin haske kan wannan batu, mataimakin babban darektan cibiyar nazarin kimiya da fasahar sararin samaniya na kasar Habasha Yishrun Alemayehu, ya bayyana cewa, tauraron dan-Adam din mai lakabin ET- Smart-RSS wanda aka harba shi a ranar Talata daga tashar harba taurarin dan-Adam dake Wenchang na kasar Sin, yana da na’urori na zamani, yana kuma iya daukar hotuna masu inganci matuka.

Ya kara da cewa, harba tauraron dan-Adam din, wani babban ci gaba ne ga kasar ta Habasha a fannoni da dama.

Yana mai cewa, cibiyar za ta ci gaba da kokarin kara karfinta a fannin kimiya da ci gaban bil-Adama.

Kasar Habashe ce dai ta zana fasalin tauraron dan-Adam din, yayin da tawagar injiniyoyin Habashan da Sin suka fito da cikakken fasali da tsare-tsarensa.

A watan Disamban shekarar 2019 ne dai, kasar Habasha ta harba tauraron dan-Adam dinta na farko, da aka yiwa lakabi da ETRSS-1 tare da taimakon gwamnatin kasar Sin.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!