Ministan Harkokin Wajen Kasar Qatar Ya Yi Kira Da A Bude Tattaunawa Kai Tsaye Tsakanin Larabawan Yankin Tekun Pasha Da Iran
2020-12-23 20:17:10

Ministan harkokin wajen na kasar Qatar Muhammad Bin Abdurrahma ali-thani wanda yake ziyarar aiki a kasar Rasha, ya ce; Tattaunawa a tsakanin kasashen yankin tekun pasha da Iran wani abin maraba da shi ne, domin zai taimaka wajen kara tabbatar da tsaro a cikin wannan yankin.
Har ila yau,
ministan harkokin wajen na Qatar ya ce; Mu da kasar Rasha bakinmu ya zo daya
wajen ganin an bai wa zaman lafiya
muhimmanci a cikin wannan yankin.
A nashi
gefen kuwa ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov,wanda ya gabatar
da taron manema labaru na hadin gwiwa da takwaran nasa na Qata, ya ce ziyarar
da tawagar da kasar Qatar ta kai zuwa Moscow za ta bayar da damar bunkasa alaka
a tsakanin bangarorin biyu ta fuskoki da dama.
Danagne da
kulla alaka da wasu kasashen Larabawa su ke yi da HKI kuwa, Lavrov ya ce; haka
baya nufin yin wancakali da hakkokin palasdinawa.
013
Tags:
ministan harkokin wajen kasar qatar
muhammad bin abdurrahma ali-thani
a bude tattaunawa tsakanin larabawa da iran
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!