Gwamnatin Najeriya Ta Kara Wa’adin Makwanni 3 Na Lokacin Rufe Hada Layin Waya Da Katin Dan Kasa

2020-12-22 22:23:51
 Gwamnatin Najeriya Ta  Kara Wa’adin Makwanni 3 Na Lokacin Rufe Hada Layin Waya Da Katin Dan Kasa

Hukumar Sadarwa ta Kasa a Nigeriya ta fitar da sanarwar karin makwanni uku daga 31 ga Disamba har zuwa 19 ga watan Janairu mai zuwa ga wanda yake da katin zama dan kasa amma bai hada shi da layin wayar sa ba.

Kuma an kara wa’adin Makonni 6 ga wadanda ba su da katin zaman dan kasa daga 31 ga Disamba zuwa 9 ga Faburairu sabuwar shekara mai kamawa, da su gaggauta yin katin sannan su hada shi da layin su.

Wannan matakin ya zo ne bayan rahotanni da aka samu na irin yadda masu son yin rajistar katin zama dan kasa suka yi dandanzo a ofishin hukumar NIMC, dake Lagos domin ganin sun yi katin kafin cikar wa’adin da gwamnati ta diba na rufe layukan wayar da ba’a yi rijistar ta da katin dan kasa ba.

A nasa bangaren shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa ma’aikatar Sadarwa ta kasa game da sabon tsarin da ta bullo da shi na kokarin hada layin waya da katin zama dan kasa.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!