​Trump Na Hankoron Sama Wa Muhammad Bin Salman Kariya Ta Doka A Amurka

2020-12-22 14:05:05
​Trump Na Hankoron Sama Wa Muhammad Bin Salman Kariya Ta Doka A Amurka

Jaridar Washington Post ta kasar Amurka ta bayar da rahoton cewa, shugaban kasar ta Amurka Donald Trump yana ta hankoron ganin ya sama wa yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya kariya ta doka, kafin ya bar mulki daga nan zuwa 20 ga watan janairu mai kamawa.

Jaridar ta ce, ta samu cikakkun bayanai na sirri kan yadda ma’aikatar harkokin wajen Amurka take ta kai gwabro tan kai mari, domin ganin ma’ikatar shari’a ta fitar da wani kudiri da zai hana gurfanar da Muhammad Bin Salman a cikin kotunan kasar.

Wannan na zuwa ne sakamakon karar da tsohon babban jami’in tsaron kasar ta Saudiyya da ya balle daga masarautar Sa’ad Al-jubbari ne ya shigar a kotun Amurka, inda ya zargi Bin Salman da yunkurin yi masa kisan gilla irin na Jamal Khashoggi, inda ita kuma Amurka ta bayar da sammaci a kan Bin Salman.

Trump na kokarin ganin kotun tarayya ta Amurka ta fitar da kudirin da zai hana gurnar da Bin Salman ne kafin ya bar mulkin Amurka nan da makonni uku masu masu zuwa, domin fitar da irin wannan kudiri a lokacin mulkin Joe Biden zai wahala matuka.

Joe Biden dai ya sha alwashin tabbatar da cewa an yi sahihin bincike kan kisan Jamal Khashoggi, da kuma hukunta dukkanin wadanda suke da hannu a cikin lamarin, yayin da shi kuma Sa’ad Jubbari wanda bababn jami’in tsaro nea bangaren leken asiria Saudiyya da ya gudu ya koma kasar Canada, yana dauke da bayanan sirri kan kisan Khashoggi, wanda dalilin hakan ne yasa ake zargin Muhammad Bin Salman na yunkurin halaka shit un kafin ya fallasa bayanan da suke a hannunsa.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!