Iran Ta Bi Sahun Kasashen Da Suka Hana Zirga-zirgar Jiragen Sama Zuwa Biritaniya

2020-12-22 09:58:13
Iran Ta Bi Sahun Kasashen Da Suka Hana Zirga-zirgar Jiragen Sama Zuwa Biritaniya

Iran, ta bi sauren kasashen yankin dama na duniya wajen dakatar da zirga zirgar jigaren sama zuwa Biritaniya, bayan bullar wani sabon nau’in cutar korona.

Da yake sanar da hakan karamin ministan sufiri na kasar, ya ce bisa umarnin ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar, dukkan zirga zirgar jiragen sama an dakatar dasu na tsawon makonni biyu, domin hana yaduwar cutar da kuma kare lafiyar al’umma.

Tun dai bayan da hukumomin Biritaniya suka sanar da bullar sabon nau’in annobar ta korona ne, kasashen duniya da dama musamman na Turai suka haramta, zirga zirgar

jiragen sama tsakaninsu da Biritaniyar.

Fiye da kasashe 40 ne na duniya suka dauki irin wannan mataki.

Hukumomin Biritaniya dai sun ce sabon nau'in cutar ta korona ya yadu cikin sauri a Landan da kuma Kudu maso Gabashin Ingila.

A nata bangare hukumar Lafiya ta Duniya Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta nemi sanar da duniya yadda ainihin lamarin yake.

Shugaban sashen samar da taimakon gaggawa na hukumar Mike Ryan ya ce kowace kwayar cuta na sauyawa daga nau'i zuwa nau'i, kuma wannan ba yana nufin tafi karfin masana kiwon lafiya ne ba.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!