Korona : Kasashen Duniya Na Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Sama Da Biritaniya

2020-12-21 14:44:26
Korona : Kasashen Duniya Na Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Sama Da Biritaniya

Kasashen duniya da dama musamman na Turai na haramta, zirga zirgar jiragen sama tsakaninsu da Biritaniya bayan bullar wani sabon nau'i na cutar korona.

Ireland, Italiya, Belgium da Netherlands duk sun haramta zuwan jirage daga Birtaniya a wani mataki na dakile yaduwar cutar a kasashensu.

Kazalika an dakatar da jiragen kasa daga Birtaniya zuwa Belgium.

Jamus da Italiya su ma sun irin wannan mataki, yayin da ita ma Faransa ta rufe filayen jiragenta ga Biritaniya na tsawon kwanaki biyu kafin ta ga abunda hali ya yi.

Hukumomin Biritaniya dai sun ce sabon nau'in cutar ta korona ya yadu cikin sauri a Landan da kuma Kudu maso Gabashin Ingila.

A nata bangare hukumar Lafiya ta Duniya ta kira da a ci gaba da tsaurara matakan dakile yaduwar cutar sakamakon sanarwar ta Biritaniya a game da sabon nau’in wannan cuta ta Coronavirus.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!