Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Jinjina Wa Ma’akatan Jinya Game Da Sadaukarwar Da Suke yi Don Ceton Al'umma
2020-12-20 20:50:12

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamina’i ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da ya gabatar a yau, don tunawa da ranar ma’aikatan jinya ta kasar, wadda ake ba ta muhimmanci matuka a kasar Iran.
Jagoran ya ce babu shakka ma’aikatan jinya suna da matsayi na
musamman a cikin kowace al’umma ta duniya, amma a wannan karo hakikanin
matsayinsu na masu sadaukarwa domin ceton rayuwar al’umma ya kara bayyana a
wannan lokaci da ake fama da annobar cutar corona.
Haka nan kuma ya bayyana cewa, baya ga aiki na kula da marasa lafiya da yi musu magani, suna da wani aiki mai muhimmanci, wanda shi ne karfafa marasa lafiya tare da sanya su cikin nishadi, domin rage musu damuwar da suke ciki, wanda wannan shi ne abin da musulunci ya yi umarni da shi.
Daga karshe jagoran ya yi fatan alhairi ga dukkanin al’ummar
kasar musamman masu sadaukarwa domin sauran al’umma su ci gaba da rayuwa a
cikin koshin lafiya, wanda kuma ma’aikatan jinya da likitoci da sauran
bangarori na kiwon lafiya suna gaba a wannan bangare.
Tags:
jagoran juyin musulunci na iran
ayatullah sayyid ali khamina’i
ranar ma’aikatan jinya ta kasar
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!