​Tsohon shugaban kasar Burundi Buyoya ya rasu bayan fama da cutar Korona

2020-12-19 14:38:04
​Tsohon shugaban kasar Burundi  Buyoya ya  rasu bayan fama da cutar Korona

A wata sanarwa da iyalan mamacin suka fitar ta nuna cewa tsohon shugaban kasar ta Burundi Pierre Buyoya ya rasu ne a birnin Paris na kasar Faransa bayan ya kamu da cutar korona Virus yana dan shekaru 71 da haihuwa, mako guda bayan daya sanar da sauka daga mukamin manzon musamman na kungiyar AU a kasahena Mali da yankin sahel

Boyoya ya taka muhummiyar rawa wajen tabbatar da mulkin demukoradiya a karamar kasar ta Afrika, sai dai a ana zarginsa da hannu wajen kisan da aka yi wa wanda ya gajeshi a mulki, kuma an yanke masa hukunci a baya idonsa tare da wasu sosjoji guda 20 da fararen hula, wasu kuma aka yanke musu hukumcin zama gidan yari na shekaru 20.

Buyoya daya fito daga kabilar tusti ya fara aikin soja ne kafin daga bisani ya juyin mulki ya dare mulki a shekara ta 1987, kana ya sake zama shugaban kasa bayan wani juyin mulki da aka yi a shekara ta 1996 suwa 2003

A shekara ta 2000 ya sanya hannun kan yarjejeniyar sulhu a birnin Arush da ta kawo karshen yakin basasan kasar da ya jawo rasa rayukan mutane 300,000 tsakanin shekarata 1993 zuwa 2006 kuma ya sauka daha kan mulkin kasar a shekata 2003 kamar yadda aka kulla yarjejeniya akai.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!