Ana Zaman Dar-dar Gabanin Babban Zabe A Afrika Ta Tsakiya

2020-12-19 14:38:00
Ana Zaman Dar-dar Gabanin Babban Zabe A Afrika Ta Tsakiya

Al’amuran tsaro a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, na ci gaba da tabarbarewa a yayin da ya rage kwanaki tara a je babban zaben kasar.

A ranar Laraba data gabata gungun masu dauke da makamai da dama a kasar sun gargadi shugaban kasar Faustin Archange Touadera, akan kada ya kuskura ya shirya zabubukan kasar.

Lamarin dai ya biyo bayan haramtawa tsohon shugaban kasar François Bozizé, tsayawa takaara a zaben shugabancin kasar.

Tuni dai MDD, ta sanar da aikewa da tawagar wanzar da zaman lafiya, wacce ke cikin shirin ko ta kwana bayan jerin hare haren da aka kaiwa wasu yankunan yammacin kasar ta Afrika ta tsakiya.

A ranar 27 ga watan nan ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa gami dana ‘yan majalisar dokoki a kasar ta Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!