Shugaba Muhammadu Buhari Na Nigeriya Ya Bada Umarnin Bude Iyakokin Kasar Na Kan Tudu Guda Hudu Da Gaggawa

2020-12-17 10:22:51
Shugaba Muhammadu Buhari Na Nigeriya Ya Bada Umarnin Bude  Iyakokin Kasar Na Kan Tudu Guda Hudu Da Gaggawa

A wata Sanarwar da Ministar Harkokin Kudi, Zainab Ahmed ta bayyanawa manema labarai bayan kammala taron Majalisar Zartarwa a jiya Laraba a Fadar Shugaban Kasa, ta ce shugaba Buhari ya bada umarnin bude dukkkan iyakokin kasar na kan tudu guda 4 sai dai har yanzu ba’a janye haramcin shigo da shinkafa, kaji da sauran dukkanin kayayyakin da aka hana shigowa da su ba.

Iyakokin kasar na kan tudu da aka amince a bude, sune na Seme da ke Lagos zuwa Kwatano, da kuma ta Ilela da ke kan iyakar Sokoto da Jamhuriyar Nijar, sai kuma ta Maigatari da ke kan iyakar jihar Jigawa da Jamhuriyar Nijar, sai kuma ta Mfun da ke kan iyakar Kudu Maso Kudu.

Sai dai Shugaba Buhari ya halarci taron ne ta bidiyo daga gidan sa dake Daura inda ya ke hutun mako daya. Kuma za’a bude sauran iyakokin kafin nan da ranar 31 Ga Disamba shekara ta 2020.

Wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da shugaban yake fuskantar suka mai tsanani game da sace daliban makarantar kwana ta garin kankara su 333 da yan bindiga suka yi .

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!