Jagora: Fitar Da Sojojin Amurka Daga Gabas Ta Tsakiya Babban Martani Ne Kan Kisan Qasem Sulaimani

Jagoran juyin juya halin musulunci a
Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, fitar da sojojin Amurka
daga yankin gabas ta tsakiya, babban martani ne kan kisan janar Qasem
Sulaimani.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau,
inda yake tabbatar da cewa, babu makawa Iran za ta mayar da martani kan kisan
Qasem Sulaimani a lokaci da kuma wurin da ta ga ya dace domin yin hakan, kamar
yadda kuma martanin zai shafi wandanda suka bayar da umarnin yin hakan, da kuma
wadanda suka aiwatar.
Dangane da batun janye takunkumai a
kan Iran ya ce bas hi da wata matsala kan hakan, idan gwamnatin kasar ta ga akwai
hanya mafi sauki domin aiwatar da hakan,
amma bai kamata a amince da yaudarar makiya ba.
Haka nan kuma ya bayyana cewa, yana
yin yin kira ga jami’an gwamnatin kasar, su mayar da hankali ne wajen rusa
takunkuman da aka drawa kasar, maimakon mayar da hankali wajen neman janye su.
Jagoran juyin juya halin na Iran ya ya
kara da cewa, Amurka ta kashe fiye dad ala biliya bakawai domin rusa kasashen
Syria da Iraki, amma burinsu bai cika ba har yanzu, kuma ba zai cika ba.
Dangane da kasashen turai uku da
suke cikin yarjejeniyar nukiliya tare da Iran, wato Jamus, Burtaniya da
Faransa, ya bayyana su da cewa da cewa kasashe ne masu tsabar munafunci da
yaudara.
015