​Mai Yiwuwa Ozil Ya Ci Gaba Da Wasa A Arsenal

2020-12-16 18:33:46
​Mai Yiwuwa Ozil Ya Ci Gaba Da Wasa A Arsenal

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bude kofar dawowa tawagar ga shahararren dan wasan tsakiyar kungiyar, Mesut Ozil a watan Janairu sakamakon halin da kungiyar ta shiga a daidai wannan lokaci.

Jaridar Leadership ta bayar da rahoton cewa, tun a watan Maris Arteta ya soke sunan tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Jamus din daga jerin ‘yan wasan da za su yi wa Arsenal wasa a gasar Firimiyar Ingila da Europa saboda wasu dalilai nasa wadanda bai bayyana ba.

Sai dai a tsakankanin wannan matsalar, Ozil ya shiga takun saka da hukumomin kungiyar, wadanda suke ganin ya ci musu fuska, bayan da ya ce zai dau nauyin biyan albashin wani ma’aikacin Arsenal mai shigar barkwanci ya yin wasannin kungiyar, wato Gunnersaurus, wanda suka sallama a farkon wannan shekarar a ya yin da suke rage yawan kudaden da suke kashewa a kungiyar saboda matsalar tattalin arzikin da annobar Korona ta taho da shi.

Kwantiragin Ozil za ta kare a karshen wannan kaka, amma Arteta na cewa akwai yiwuwar tattaunawa da shi a watan Janairu idan da hali zai iya komawa fili domin ci gaba da bugawa kungiyar wasa kamar yadda yake a baya.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!