Kasar Somaliya Ta Sanar Da Yanke Huldar Diplomasiyya Da Kasar Kenya

2020-12-15 14:52:24
Kasar Somaliya Ta Sanar Da Yanke Huldar Diplomasiyya Da Kasar Kenya

Sanarwar gwamnatin ta Somaliya akan yanke huldar da Kenya, ta kuma kunshi bai wa makwabciyar tata wa’adin mako guda da ta janye jami’an diplomasiyyarta daga tata kasar.

Gwamnatin Somaliya dai ta zargi kasar Kenya da tsoma baki a harkokin siyasar kasarta.

Dama dai a alaka a tsakanin kasashen biyu ta dade tana samun tangarda, inda a wata daya da ya gabata Somaliyan ta kira yi jakadanta daga Nairobi, tare da korar jakadan Kenya daga Magadishu.

Zargin da Somalia take yi wa Kenya, y akunshi tsoma baki a harkokin zaben da aka gudanar a yankin Jubaland wanda daya ne daga cikin yankunan Kasar Somaliya 5 masu kwarya-kwarya cin gashin kai.

A shekaru baya, kasar Kenya ta aike da sojoji zuwa cikin kasar Somalia domin yakar kungiyar Al-Shabab, sai dai ba a je ko’ina ta janye su bayan wani mummunan hari da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan sojojin nata.

Har ila yau kungiyar ta Al-Shabab ta rika kai hare-hare a cikin kasar Kenya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa, a cikin cibiyoyin kasuwanci da kuma na ilimi.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!